Yara biyar sun rasa rayukansu yayin da wani ya jikkata sakamakon rushewar wata katanga a yankin Bulumkutu da ke Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na yammacin Lahadi, 4 ga Janairu, 2026.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya bayyana cewa katangar ta rushe ne a kan yara shida da ba su haura shekaru 16 ba. Ya ce yara biyar sun mutu nan take, yayin da ɗaya ya samu rauni kuma yana karɓar magani a asibiti.
’Yan sanda sun ce sun fara bincike domin gano musabbabin afkuwar lamarin. Daso ya kuma shawarci jama’a da su kula da ingancin gine-gine tare da sanya ido sosai kan yara domin kauce wa irin wannan mummunan lamari.
