Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya karyata ikirarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya. Soludo ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a Kudu maso Gabas ba na addini ba ne, illa dai rikici ne tsakanin ’yan uwa Kiristoci da ke cikin yankin.

Yayin wata hira kai tsaye da tashar Channels Television, Soludo ya ce kalaman Trump suna iya tada husuma, inda ya jaddada cewa mutanen da ke cikin dazukan yankin — wadanda ke kashe mutane — su ma Kiristoci ne. Ya ce, “Sunayensu Emmanuel, Peter da John ne. Wannan rikici ba tsakanin Kiristoci da Musulmai ba ne.”

Gwamnan ya kara da cewa kusan kashi 95 cikin 100 na mutanen Kudu maso Gabas Kiristoci ne, don haka ba za a ce ana kisan Kiristoci saboda addini ba. A cewarsa, matsalar ta samo asali ne daga siyasa, tattalin arziki, da rashin sulhu tsakanin al’ummar yankin.

Soludo ya roki Amurka da sauran kasashe su daina kallon rikicin Najeriya ta fuskar addini, su kuma tallafa wajen samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da sulhu. Ya tabbatar da cewa Najeriya za ta shawo kan matsalolinta idan aka mayar da hankali kan tushen rikicin, ba a karkatar da hankali zuwa addini ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version