Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa abin takaici ne kuma abin damuwa ƙwarai jin labarin sace ɗalibai mata 25 a Jihar Kebbi da kuma kisan Brigediya Janar Musa Uba tare da wasu sojoji a Jihar Borno. Ya ce yana mika ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, tare da roƙon Allah ya basu juriya da ta’aziya.
Tinubu ya ce ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kai dauki domin dawo da ɗaliban Kebbi, yana mai jaddada cewa ya san da ƙaruwa hare-haren ’yan ta’adda a sassa daban-daban na ƙasar. Ya bayyana cewa dole ne jami’an tsaro su mayar da martani cikin hanzari, ƙwazo da kuma ƙarfi domin kare al’umma.
A cewar rahotanni, ’yan bindiga dauke da makamai sun mamaye makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School da misalin ƙarfe huɗu na asuba sannan suka sace ɗalibai 25 daga ɗakunan kwana. Lamarin ya sake tunzura al’umma, musamman ganin cewa irin wannan hari ya maimaita tun bayan sace ’yan matan Chibok sama da shekara goma da ta wuce.
Tinubu ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen tsare rayuka da kare yara. Ya gargadi masu tayar da hankali cewa za su fuskanci cikakken hukunci daga gwamnati, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta lamunci barazanar tsaro ba ko kaɗan.
