Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta bukaci mazauna jihar da su tabbatar sun mallaki izinin gini kafin fara duk wani aikin gini, domin bin ka’idojin gine-gine da aka amince da su na da matuƙar muhimmanci wajen dakile rugujewar gine-gine da kare rayuka da dukiyoyi.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Bahijja Malam Kabara, ta ce Mukaddashin Daraktan Gudanarwa na KNUPDA, Tpl. Nura Maude, ne ya yi wannan kira yayin da yake duba gine-ginen da suka ruguje a wasu sassan Kano, ciki har da Ƙaramar Hukumar Tarauni da Kurna da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.
Hukumar ta ce rugujewar gine-ginen ta yi sanadin asarar rayuka, jikkatar wasu mutane da kuma lalata dukiyoyi. Tpl. Nura Maude ya bayyana cewa samun izinin gini na daga cikin muhimman matakan tabbatar da tsaro, domin yana tabbatar da cewa gine-ginen sun cika ƙa’idojin tsara birane, tsarin gini da muhalli.
Ya kuma gargadi masu gidaje da masu amfani da gine-gine cewa rashin bin ƙa’idojin gini na iya jefa masu gidaje, mazauna gine-gine da al’ummomin da ke makwabtaka da su cikin babban haɗari, wanda zai iya haifar da jikkata, asarar rayuka da dukiyoyi.
