Wata babbar kotu a birnin Kuala Lumpur na ƙasar Malaysia ta yanke wa wani ɗan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same shi da laifin kashe ɗan jikansa. Kotun ta ce mutumin, mai suna Ibekwe Emeka Augustine, ya jefo yaron mai shekara huɗu daga bene na uku na wani gini a shekarar 2020.
Alƙali K. Muniandy ya ce hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da laifin, inda aka tuhumi Augustine da aikata kisan ne tsakanin ƙarfe 7:45 zuwa 8:15 na safe a ranar 29 ga Nuwamba, 2020. An gurfanar da shi ne ƙarƙashin sashe na 302 na dokar laifuka, wadda ta tanadi hukuncin kisa ko ɗaurin shekaru masu yawa.
Baya ga hukuncin kisa, kotun ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar bisa wasu laifuka huɗu da suka haɗa da yunƙurin kashe ɗansa, raunata matarsa, yunƙurin kashe kansa da kuma cin zarafin ’yarsa. Hukuncin ɗaurin zai gudana ne a lokaci guda, kamar yadda kotun ta bayyana.
