Kotu Ta Bayar da Umarnin Kama Tsohon Shugaban PDP
Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ɓangare, Kabiru Turaki, bisa gaza halartar kotu domin gurfana a shari’ar da ‘yan sanda suka shigar a kansa. Alkalin kotun, Mai shari’a U.P. Kekemeke, ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis 26 ga Maris, 2026.
Kotun ta bayyana cewa babu wani dalili da ya sa Turaki bai halarci zaman kotun ba, inda ta umurci a kamo shi a gabatar da shi domin fara shari’a. Ana tuhumarsa ne da bayar da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda a wata ƙara da aka shigar tun a watan Oktoban 2022.
Lauyan wanda ake ƙara ya shaida wa kotun cewa rashin halartar Turaki ya biyo bayan wata takarda da ya aikewa babban alkalin kotun yana neman a canja alkalin shari’ar. Sai dai kotun ta ce hakan ba zai dakatar da shari’a ba, inda ta amince da bukatar masu gabatar da ƙara tare da dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci.


