Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja karkashin Mai Shari’a Muhammad Umar ta bayar da umarnin tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, a Gidan Gyaran Hali na Kuje har zuwa lokacin da za a saurari bukatarsa ta soke umarnin da ya janye belinsa.

A zaman kotun na ranar Litinin, Sowore ya bayyana tare da sabon lauyansa, Olumide Fusika (SAN). Tun a zaman da ya gabata ne kotun ta janye belinsa bayan ya kasa halartar shari’a, lamarin da ya sa masu gabatar da kara suka zarge shi da jinkirta shari’ar.

Mai Shari’a Umar ya kuma yi watsi da bukatar Sowore na janye kansa daga sauraron karar bisa zargin nuna son kai. Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga Yuni, yayin da Hukumar DSS ke tuhumarsa da wallafa bayanan da ake zargin karya ne kan Shugaba Bola Tinubu a shafukansa na X da Facebook.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version