Babbar Kotun Jihar Kano mai sauraron ƙorafe-ƙorafen ɗaukaka ƙara ta saurari ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar, yana ƙalubalantar hukuncin kisa da Kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu ta yanke masa kan zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
A zaman kotun da aka gudanar, lauyoyin ɓangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu, inda lauyoyin Sheikh Abduljabbar suka roƙi kotun ta soke hukuncin da aka yanke masa tare da wanke shi daga zargin. Sai dai lauyoyin gwamnatin Jihar Kano sun buƙaci kotun ta tabbatar da hukuncin da aka yanke a shari’ar farko.
Mai Shari’a Nasir Saminu ya umarci a gabatar masa da litattafan da aka yi amfani da su wajen kafa hujja a shari’ar farko domin ci gaba da nazarin ƙarar. BechiHausa ta ruwaito cewa kotun za ta sanar da ranar yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar a wani lokaci mai zuwa.
