Kotun Kwadago ta Ƙasa da ke Abuja ta umarci United Bank for Africa (UBA) ta biya tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kogi, Simon Achuba, kuɗaɗen hukuncin da ya kai N1.07bn bayan ta tabbatar da cewa akwai isassun kuɗaɗe a asusun ACRESAL na jihar. Alƙali R. B. Haastrup ya zartas da hukuncin ne bayan ya ce UBA ta kasa gabatar da takardun da za su tabbatar da cewa kuɗin na tallafin Bankin Duniya ne ko na jihohi 19 na Arewa.
A zaman da aka yanke hukuncin a ranar 27 ga Nuwamba, Achuba ta hannun lauyansa Femi Falana (SAN), ya nemi a maida umarnin garnishee absolute, ganin cewa bankin ya amince da wanzuwar kuɗin a asusun dalar. UBA ta dage cewa kuɗin an tanada su ne domin aikin muhalli, don haka ba za a iya amfani da su wajen biyan bashin hukunci ba, amma kotu ta yi watsi da wannan kariya saboda babu wani shaida mai ƙarfi da aka gabatar.
A cikin hukuncin, kotun ta ce doka ba ta yarda a hana mai nasara cin moriyar hukuncinsa ba idan aka tabbatar da wanzuwar kuɗi. A nan, Bechi Hausa ta gano cewa kotu ta umarci UBA ta biya N1,070,860,138 tare da ƙarin N2m da kotun ɗaukaka ƙara ta ware masa da kuma N1m kuɗin shari’ar sa.
Haka kuma kotu ta sallami sauran bankuna da aka shigar a shari’ar, tare da hukunta lauyan gwamnatin Kogi, Paul Daudu (SAN), da biyan N1m saboda ɗabi’a mara kyau da kotu ta ce tana ƙoƙarin karkatar da doka. Wannan hukunci ya zama babbar nasara ga Achuba a rikicinsa da gwamnatin Kogi tun bayan tsige shi da aka yi a 2019.
