Babbar Kotun Jihar Sakkwato ta yanke wa wasu mutum uku, ciki har da wani ɗan ƙasar Nijar, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifukan ta’addanci da safarar makamai ba bisa ka’ida ba.
Wadanda aka yankewa hukuncin sun haɗa da Yusuf Muhammad (Sallau), Jabbi Alhaji Yalle da Kabiru Muhammad, waɗanda jami’an Hukumar DSS suka kama a ranar 13 ga Yunin 2025 bisa zargin aikata laifukan da suka shafi ta’addanci, safarar makamai da laifukan da suka shafi iyakokin ƙasa.
Mai shari’a Bello ya same su da laifukan da ake tuhumarsu da su tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Kotun ta kuma umarci a kwace dukkan kuɗaɗen da aka samu daga hannunsu tare da mika su ga Gwamnatin Tarayya.
