Madugun tafiyar Kwankwasiyya kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ayyana ranar 23 ga watan Janairu na kowace shekara a matsayin ranar “butulci” ta duniya.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wani taro da yake ci gaba da gudanarwa na karɓar ziyara daga ƙungiyoyin Kwankwasiyya, inda ya ce ya ɗauki matakin ne a matsayinsa na jagoran tafiyar.
Ya ce ayyana ranar na da nufin tunatarwa da faɗakarwa kan muhimmancin biyayya da godiya a tafiyar siyasa, tare da jan hankali kan illar butulci ga haɗin kai da ci gaban al’umma.


