‘Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Garin Idi da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka yi garkuwa da mutum sama da 50. Ƙauyen shi ne mahaifar Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir.
Mazauna garin sun ce maharan sun shiga ƙauyen da daddare, suka rabu gida biyu, inda wani rukuni ya sace kusan mata 30, yayin da ɗayan ya yi garkuwa da almajirai sama da 20 daga wata makarantar allo.
A cewar mazauna ƙauyen, bayan tattaunawa da shugabannin al’umma, maharan sun buƙaci a biya Naira miliyan ɗaya domin a saki matan da kuma Naira 600,000 domin sauran mutanen da suka kama. Bayan an biya Naira 600,000, sun saki almajiran amma suka ci gaba da riƙe matan.
Maharan sun sake dawowa washegari, inda suka tilasta wa ƙauyen biyan Naira 300,000 a matsayin haraji tare da barazanar sake yin garkuwa da mutane idan ba a biya ba. Sai dai kakakin ‘yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce ba su da cikakken bayani kan harin domin ba a kai musu rahotonsa ba.
