Matatar Man Dangote ta dawo sayar da fetur da Naira, inda ta kawo ƙarshen amfani da dalar Amurka wajen sayar da man. Haka kuma ta ƙara farashin litar fetur daga N1,075 zuwa N1,215, wanda ya nuna ƙarin N140.

Matatar ta sanar da sauyin farashin ga ‘yan kasuwa a ranar Laraba, tare da bayyana cewa sabon farashin ya fara aiki nan take. Haka kuma ta buƙaci kwastomomi su ci gaba da yin odar man fetur.

Matatar ta dakatar da sayar da fetur da Naira a ranar 15 ga Yuli bayan ta koma amfani da dalar Amurka saboda ƙarancin ɗanyen mai da take samu ƙarƙashin shirin musayar Naira da ɗanyen mai na Gwamnatin Tarayya. Sai dai gwamnatin tarayya ta shiga tsakani bayan korafin masu kasuwancin man fetur.

Rahotanni sun nuna cewa dawowar sayar da fetur da Naira za ta taimaka wajen sauƙaƙa rabon man fetur a ƙasar. Duk da haka, sabon farashin na N1,215 kan kowace lita na iya haifar da ƙarin farashin fetur a gidajen mai idan ba a samu sauyin farashin ɗanyen mai ko gasa a kasuwa ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version