Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da buƙatar ƙirƙirar sabbin jihohi guda shida. Wannan na daga cikin manyan matakai da aka cimma a cikin shirin sauya tsarin mulki da ake gudanarwa a halin yanzu.

Matsayar ta fito ne a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu da aka gudanar a jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da kuma mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu.

A yayin taron, kwamitin ya tattauna kan buƙatu guda 69 da suka haɗa da ƙirƙirar jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Bayan doguwar muhawara da nazari, an cimma matsaya kan amincewa da ƙirƙirar jihohi guda shida, ɗaya daga kowace shiyya ta ƙasar.

Idan wannan shawara ta sami amincewar majalisun biyu da kuma sahalewar shugaban ƙasa, Najeriya za ta ƙaru daga jihohi 36 zuwa 42, abin da zai zama tarihi a tsarin siyasar ƙasar tun bayan kafa tsarin mulki na 1999.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version