Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi bayan doguwar muhawara da aka shafe shekaru ana yi a kai. Kudirin, wanda ke neman yin kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulki na 1999, ya samu amincewar majalisar bayan karatu na farko, na biyu da na uku.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce kudirin zai ba jihohin da suka amince damar kafa rundunar ’yan sandansu, tare da ci gaba da barin rundunar ’yan sandan tarayya ta gudanar da ayyukanta. Ya kuma ce an tanadi matakan kariya domin hana amfani da rundunar wajen siyasa ko tauye haƙƙin jama’a.
Kudirin zai ci gaba da matakai na doka, inda ake sa ran Majalisar Wakilai za ta daidaita sigarsa kafin a tura shi ga majalisun dokokin jihohi domin amincewa. Idan ya samu goyon bayan aƙalla jihohi 24 daga cikin 36, za a miƙa shi ga Shugaba Bola Tinubu domin sanya hannu ya zama doka.
