A ranar Laraba, 26 ga Nuwamba 2025, misalin ƙarfe 16:04 na yamma agogon WAT, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya sanar da nadin jakadu uku na musamman (non-career ambassadors), lamarin da ya kawo ƙarshen kusan shekaru biyu ana jiran wannan mataki. Sun haɗa da Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jigawa da Ayodele Oke daga Oyo. An tura sunayen zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa, inda Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya ce yanzu sunaye uku ne amma ana sa ran ƙarin wasu daga baya.
Nadin ya zo bayan suka da damuwa daga wasu ‘yan Najeriya musamman bayan gwamnatin Donald Trump ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kula da su saboda rashin naɗa jakadu. Sai dai tun watan Satumba, Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya jaddada cewa ofisoshin jakadanci suna aiki yadda ya kamata ta hannun chargé d’affaires da sauran jami’an diflomasiyya. Ya bayyana cewa tsarin diflomasiyya ba na mutum guda ba ne, akwai mataimaka, masu ba da shawara da sauran ƙwararru da ke tafiyar da harkokin yau da kullum.
A cewar sa, naɗin jakadu haƙƙin shugaban ƙasa ne kuma zai kasance a lokacin da ya dace, yayin da ayyukan kare muradun Najeriya a ƙasashen waje ke ci gaba. BECHI HAUSA ta tattaro cewa ministan ya ce ofisoshin jakadancin Najeriya na ci gaba da tallafa wa ‘yan ƙasar wajen harkokin kasuwanci, zuba jari, al’adu da ayyukan takardun shaida, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne sakamako, ba wai kyan gani na zahiri ba.


