Wasu ƴan bautar ƙasa shida a Anambra sun shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Awka, suna neman gwamnatin jihar ta biya su diyya ta naira biliyan ɗaya saboda duka da tsare su da ake zargin jami’an kungiyar tsaron sa-kai ta Agunechemba suka yi musu. Wadanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Jennifer Elohor, Greatness Oyeh, Eze Ikenna, Anighoro Godspower, Feyisara Amore, da Chimenum Wonodi.

Rahotanni sun bayyana cewa a watan Agusta wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga jami’an Agunechemba suna bugun wasu daga cikin waɗannan ƴan NYSC bayan sun shiga gidan da suke haya. An ce ɗaya daga cikinsu, Elohor, an yi mata duka har an tube mata kaya, duk da cewa sun nuna katin shaidar NYSC ɗin su.

Ƴan bautar ƙasar sun shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansu, Cyrus Onu, inda suka sanya Gwamnatin Jihar Anambra, Gwamna Chukwuma Soludo, Atanurajen Jihar, da Kungiyar Vigilante a matsayin waɗanda ake ƙara. Sun nemi kotu ta bayyana cewa kama su, tsare su, da duka da suka sha sun sabawa kundin tsarin mulkin ƙasa da ‘yancin dan Adam.

Sannan kuma, sun roƙi kotu ta tilasta wa gwamnati da sauran waɗanda ake ƙara su bayar da gafara a rubuce, a wallafa ta a manyan jaridun ƙasa biyu da ɗaya ta jihar Anambra, a matsayin diyya da gyaran sunansu daga cin mutuncin da suka sha.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version