Wasu masu zanga-zanga sun mamaye ginin Majalisar Dokoki ta tarayya a Abuja, domin nuna damuwarsu kan jinkirin tabbatar da nadin Injiniya Abdullahi Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Lantarki ta Kasa (NERC), wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sunansa zuwa Majalisar watanni da suka gabata. Masu zanga-zangar, da suka hada da kungiyoyin fararen hula da magoya bayan Ramat, sun rera wakokin hadin kai dauke da kwalaye da ke kira ga Majalisar da ta kammala tabbatar da nadin cikin gaggawa.
A cewar jagoran masu zanga-zangar, Ahmed Suleiman, Ramat ya riga ya sami amincewa daga kwamitin Majalisar da ta duba cancantarsa, amma an dakatar da nadin nasa saboda wasu “masu ruwa da tsaki” da ke kokarin hana shi shiga ofis. Ya ce akwai masu amfani da siyasa wajen yada bayanan karya domin hana shi samun wannan mukami, duk da cewa yana da gogewa da kwarewar da ake bukata a bangaren wutar lantarki.
Sai dai Majalisar Dattawa ta yi watsi da zargin cin hanci da ake cewa wasu sanatoci sun ci dala miliyan 10 domin hana tabbatar da nadin Ramat. Kakakin Majalisar, Yemi Adaramodu, ya ce an dai dakatar da nadin ne saboda wasu koke-koke da aka samu daga jama’a da kuma cikin gida. Ya jaddada cewa Majalisar ba za ta yi gaggawa wajen tabbatar da kowane nade-nade ba idan har akwai abin da ke bukatar karin bincike.
Nadin Ramat dai na ci gaba da jawo cece-kuce a lokacin da kasar ke fuskantar karin farashin wutar lantarki da karancin isasshen wuta. Yanzu ana jiran ci gaba daga bangaren Majalisar Dattawa, wadda ta ce za ta cigaba da nazari kafin daukar matakin karshe.
