Matatar man fetur ta Dangote Petroleum Refinery ta sake ƙara farashin fetur, inda ta ɗaga farashin Premium Motor Spirit (PMS) zuwa naira 1,175 kan kowace lita. Karin farashin dai shi ne karo na uku cikin mako guda, lamarin da ake sa ran zai ƙara tsadar kayayyaki da hidimomi a faɗin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa matatar ta sanar da ‘yan kasuwa sabon farashin ne a ranar Litinin, inda aka ƙara shi daga naira 995 zuwa naira 1,175 kan lita, wato karin naira 180 cikin kwanaki uku kacal. Haka kuma an ɗaga farashin dizal, wato Automotive Gas Oil, zuwa naira 1,620 kan lita.

Wani babban jami’i a matatar ya tabbatar da sauyin farashin, yana mai cewa kasuwar man fetur tana fuskantar sauye-sauye masu yawa da suka shafi farashin maye gurbin kaya. Karin farashin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin fetur a wasu gidajen mai ya haura naira 1,000 kan lita, lamarin da ke ƙara matsin tattalin arziki ga ‘yan Najeriya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version