Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta yi sauki sosai, yana mai jaddada cewa gwamnatin tarayya na kokarin shawo kan kalubalen. Bwala ya bayyana hakan ne a wani shiri mai suna Head to Head na tashar Al Jazeera da dan jarida Mehdi Hasan ke gabatarwa a London, wanda aka wallafa a kafafen sada zumunta ranar Juma’a.
Bwala ya amince cewa akwai matsalar tsaro a Najeriya, amma ya ce babu wata kasa a duniya da ba ta fuskantar irin wadannan kalubale. Ya kuma ce gwamnatin Najeriya na hada kai da kasashe kamar Turkiyya da Amurka domin magance matsalar ta hanyar yarjejeniyoyi da hadin gwiwar yaki da ta’addanci.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnati na aiki dare da rana wajen dakile matsalar, yana mai cewa an kama ko an kashe wasu shugabannin kungiyoyin ta’addanci a baya. Duk da haka, rahotanni sun nuna cewa a baya-bayan nan an samu hare-haren ta’addanci da sace-sacen mutane a wasu sassan kasar, ciki har da harin da aka ce ya yi sanadin sace sama da mata da yara 100 a jihar Borno.


