Jami’ai a arewacin Najeriya sun ce sojojin kasar sun kashe ’yan bindiga 45 da suka kai hari wani kauye a jihar Katsina. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, kamar yadda hukumomin jihar suka tabbatar.

Tun da farko dai an ce ’yan bindigar da suka taso daga jihar Zamfara sun kai hari kauyen Alhazawa da ke karamar hukumar Danmusa a ranar Alhamis domin satar shanu. Sai dai mazauna kauyen sun yi turjiya inda suka kashe hudu daga cikin maharan.

Bayan kwana guda ne kuma ’yan bindigar suka sake taruwa domin daukar fansa kan mazauna kauyen, amma suka ci karo da sojoji a kan hanyarsu, lamarin da ya haifar da musayar wuta. Rahotanni sun ce an kashe sojoji uku a yayin wannan gumurzu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version