Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tsira kuma ya bar ƙasar Guinea-Bissau ta jirgi na musamman. Jonathan ya je ƙasar ne a matsayin jagoran tawagar West African Elders Forum domin sa ido kan zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisa. Amma sai sojojin ƙasar suka kifar da gwamnatin Umaro Sissoco Embaló, suka rufe iyakoki, tare da ɗaukar ikon mulki gaba ɗaya. Rikicin ya ɓarke ne yayin da ake jiran sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar 23 ga Nuwamba.

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta tattauna batun cikin gaggawa, inda mataimakin Kakakin Majalisa Benjamin Kalu ya nemi gwamnati ta tabbatar da ceto Jonathan cikin gaggawa. Shugabannin majalisa sun yaba irin rawar da ya taka wajen sa ido kan zaɓe a ƙasashe daban-daban, tare da bukatar a yi duk mai yiwuwa wajen kare lafiyarsa. Gwamnatin tarayya ta kuma yi tir da juyin mulkin, tana mai cewa matakin babban barazana ne ga damokradiyya a yammacin Afirka. Abuja ta bukaci a gaggauta mayar da tsarin mulki da sakin duk wadanda aka kame.

Jonathan, tare da tsohon shugaban Mozambique Filipe Nyusi da jagoran tawagar ECOWAS Issifu Kamara, sun fitar da sanarwa mai tsaurin kalamai kan juyin mulkin. Sun ce an yi yunkurin dakile tsarin zaɓe da kuma kwanciyar hankali na ƙasar. Bechi Hausa ta tattaro cewa an samu harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, aka kai hari ofishin Hukumar Zaɓe, yayin da sojoji suka toshe manyan hanyoyi. A halin da ake ciki, rundunar sojoji ta naɗa Janar Horta N’Tam a matsayin shugaban riƙo na shekara guda.

Guinea-Bissau na fuskantar rikice-rikicen siyasa tun bayan samun ’yancin kai, inda aka yi nasarar juyin mulki fiye da hudu. Kungiyoyin ECOWAS da AU sun yi fatali da matakin, suna mai cewa ba za su amince da karɓar mulki ta hanyar da ta sabawa kundin tsarin mulki ba. Kasashen duniya ciki har da MDD da Portugal sun bukaci a yi hattara, tare da kare ’yancin jama’a da ’yancin manema labarai. Najeriya ta ce za ta ci gaba da aiki da abokan hulɗa domin tabbatar da dawo da zaman lafiya da tsarin mulki a Guinea-Bissau.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version