Mutum 15 sun mutu bayan da suka ƙone ƙurmus, yayin da wasu 25 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Neja.
Kwamandar FRSC ta jihar, Aishatu Sa’adu, ta ce fasinjojin 15 na cikin ɗaya daga cikin motocin bas ɗin da suka yi karo, inda motar ta kama da wuta. Ta ce an kwantar da waɗanda suka jikkata a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Bida da Babban Asibitin Kutigi.
Ta ce hatsarin ya faru ne a kan hanyar Enagi zuwa Mokwa, tsakanin wasu motocin bas guda biyu, bayan da suka yi karo a wata kwana da ke yankin Duma, a Ƙaramar Hukumar Mokwa.
Kwamandar ta danganta hatsarin da ƙoƙarin wuce wata mota ba bisa ƙa’ida ba da kuma gudun wuce sa’a. Ta gargadi masu tuƙi da su kiyaye gudun da ya dace, tare da guje wa ƙoƙarin wuce motocin da ke gabansu ba bisa ƙa’ida ba.
