Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu a jihar Neja sakamakon jerin hare-hare da ramuwar gayya da ke da alaƙa da rikicin manoma da makiyaya. Rundunar ƴan sanda ta ce maharan sun kai hari ƙauyen Godoro a daren Litinin, inda suka kashe wani matashi mai shekara 25, lamarin da ya jawo mambobin ƙungiyar sa-kai suka kashe wani mutum mai shekara 28 domin ramuwar gayya.
Kakakin ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce a daren Talata kuma an ƙona mutane 15 har lahira a wani gida mai ɗakuna biyu da ke Angwan-Baago kusa da Godoro, yayin da aka kashe wani mutum a wani wuri na daban, wanda ya kai adadin waɗanda aka tabbatar sun mutu zuwa 18.
Sai dai majiyoyin yankin sun ce adadin waɗanda suka mutu na iya kaiwa 48, yayin da wani mazaunin yankin ya kiyasta cewa mutum 43 ne aka kashe. Rikicin manoma da makiyaya ya daɗe yana haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a sassan Najeriya.

