Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a jam’iyyar ADC, bayan ta yi watsi da ƙarar ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, da ya ƙalubalanci naɗin Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Mai shari’a Musa Liman ya ce kotun ba ta da hurumin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyya. Ya kuma bayyana cewa Abejide bai nuna an tauye masa wata doka ko haƙƙi ba, kuma bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikicin cikin jam’iyyar kafin ya garzaya kotu ba.
Kotun ta tabbatar da cewa miƙa shugabanci daga Ralph Nwosu zuwa David Mark ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ADC, Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma sa ido na INEC. Haka kuma, ta umarci Abejide ya biya tarar Naira miliyan biyu ga kowane wanda ake ƙara, yayin da aka ci lauyansa tarar Naira miliyan 10.

