Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, SAN, ya bayyana cewa hukumar EFCC ta kammala tambayoyinta gare shi tare da ba shi damar komawa gida. Malami ya wallafa sanarwar ne a shafinsa na Facebook bayan ya fito daga ofishin hukumar da ke Abuja.

Malami ya ce ya gode wa Allah bisa ikon da ya samu na amsa dukkan tambayoyin cikin kwanciyar hankali. Ya bayyana zaman da jami’an EFCC suka yi da shi a matsayin mai cike da mutunci da fahimtar juna, inda ya ce komai ya gudana cikin tsafta da nutsuwa.

A cewar Malami, shanun ba su kare ba domin hukumar ta sanya wani sabon kwanan wata da zai sake komawa domin cigaba da tattaunawa. Ya tabbatar wa jama’a cewa zai ci gaba da bin dukkan matakan doka. Kakaki24 ta tattara cewa wannan ne karo na farko da tsohon ministan ya fitar da cikakken bayani kan gayyatar da EFCC ta yi masa.

Tsohon ministan ya sake jaddada cewa ya amince da duk abubuwan da EFCC ke nema, yana mai cewa ya yi imani da tsarin doka da oda. Yanzu idanu sun karkata zuwa zama na gaba da hukumar ta tsara domin ci gaba da binciken da ake yi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version