Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile wani mummunan hari da ‘yan ta’adda ke shirin kaiwa a garin Chibok da ke kudancin Jihar Borno. Rundunar ta bayyana cewa ta samu bayanan sirri kan yunkurin fiye da mayaƙa 300 da ke neman kutsa garin domin kai mummunar gaba.

Sanarwar rundunar ta ce bayan samun bayanan sirri, dakarun suka kafa shirin musamman tare da kwanton ɓauna, wanda ya kai ga tarwatsa duk wani shirin mayakan tun kafin su kutsa cikin garin. An yi musayar wuta na tsawon sa’o’i biyu, lamarin da ya tabbatar da ƙwarewar sojojin wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Kakaki24 ta tattaro cewa dakarun runduna ta 28 da ta 25, tare da goyon bayan rundunar sojin sama da ta tura jiragen yaƙi na Tucano da jirage marasa matuƙa, ne suka gudanar da wannan samame. Rundunar ta tabbatar da cewa babu wani jami’in soja da ya rasa ransa ko ya jikkata a cikin artabun.

Sanarwar ta ƙara da cewa luguden wutar da sojoji suka yi ya tilasta mayaƙan ja da baya har zuwa cikin dajin Sambisa, inda ake kyautata zaton sun samu mummunar illa. Rundunar ta jaddada cewa tana ci gaba da sintiri domin tabbatar da cikakkiyar zaman lafiya a yankin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version