Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ya bar aiki ne “da cikakken kwanciyar hankali” bayan shafe kusan shekaru 40 yana hidima ga rundunar sojin Najeriya. A wurin bikin sallamarsa da aka yi a Abuja, Musa ya bayyana cewa ya yi wa ƙasa hidima da gaskiya da sadaukarwa, yana mai cewa: “Na bar aiki da zuciya ɗaya, na yi iya ƙoƙarina domin tsaron ƙasarmu.”
Janar Musa ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa ba shi damar zama Babban Hafsan Tsaro tun a shekarar 2023, yana mai bayyana wannan dama a matsayin babban girmamawa da ba zai taɓa mantawa da ita ba. Ya ƙara da cewa koda yake ya yi ritaya daga aiki, bai daina son Najeriya ba, domin “soja ne har abada, kuma ɗan ƙasa mai kishin ƙasa.”
Ya kuma ja hankalin hukumomin tsaro da sauran jami’an leken asiri da su ci gaba da haɗa kai domin yaki da matsalolin tsaro, yana mai jaddada cewa “ba wata hukuma guda da za ta iya yin wannan yaƙi ita kaɗai.” Musa ya roƙi ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’a ga sojojin da ke fagen fama domin samun nasara da zaman lafiya.
A ƙarshe, ya taya sabon Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, murna tare da neman jami’an tsaro da su ci gaba da nuna masa biyayya da ƙwarewa kamar yadda suka yi masa. Ya gode wa iyalansa bisa juriya da goyon baya, da kuma kafafen yada labarai da sauran hukumomin tsaro bisa haɗin kai da suka nuna a lokacin da yake kan mulki.
