Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana mamakinsa kan yadda Muhammadu Buhari bai kawo ƙarshen matsalar Boko Haram ba duk da cewa ƙungiyar ta taɓa zaɓar shi a matsayin wakilinta a tattaunawa da gwamnati lokacin mulkinsa.

Jonathan ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” da tsohon babban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor ya rubuta.

Ya ce gwamnatin sa ta kafa kwamiti na musamman domin tattaunawa da Boko Haram, sai suka gano cikin mamaki cewa ƙungiyar ta zaɓi Buhari a matsayin wakilinta — alamar yiwuwar sulhu. Jonathan ya ce hakan ne ya sa ya yi fatan Buhari zai kawo ƙarshen rikicin da zarar ya hau mulki a 2015.

Sai dai ya nuna takaici cewa hakan bai faru ba, domin rikicin ya ci gaba da jawo asarar rayuka da dukiya a sassa da dama na ƙasar duk da sauyin gwamnati.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version