Sabbin bayanai daga Hukumar (NMDPRA) sun nuna cewa duk da fara aikin masana’antar Dangote, Najeriya ta shigo da lita biliyan 15 na fetur daga watan Agusta 2024 zuwa farkon Oktoba 2025 — kimanin kashi 69 cikin 100 na jimillar man da ƙasar ta sha. Wannan ya faru ne duk da cewa masana’antar Dangote ta fara samar da fetur tun a watan Satumba 2024.

Rahoton ya bayyana cewa jimillar man da aka samu a ƙasar ya kai lita biliyan 21.6, inda lita biliyan 6.6 kacal aka tace a cikin gida. A cewar NMDPRA, yawan shigo da man ya ragu daga sama da miliyon 54 a rana a Satumba 2024 zuwa kusan miliyon 15 a rana a farkon Oktoba 2025, wanda ke nuna cewa Dangote na ƙara ɗaukar kaso mai yawa a kasuwa, duk da ƙalubale daga masu shigo da mai daga waje.

Sai dai rahoton ya ce duk da wannan cigaba, ƙasar har yanzu tana dogaro da man waje a mafi yawan lokuta, yayin da masana’antar Dangote ke ci gaba da samar da sama da miliyon 18 zuwa 20 a rana. A lokaci guda, Dangote na fitar da man jirgi, dizal, da fetur zuwa ƙasashen waje ciki har da Saudi Aramco da ƙasashen Gulf, abin da ke nuna ƙarfin masana’antar wajen samarwa fiye da bukatar cikin gida.

Masana sun bayyana cewa Najeriya na cikin sabon mataki na canjin tsarin samar da man fetur, daga dogaro da shigo da mai zuwa ci gaba da tacewa a cikin gida, wanda zai iya kawo ƙarshen dogon tarihi na dogaro da man waje idan aka ci gaba da tallafawa masana’antun cikin gida kamar ta Dangote.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version