Hukumar shirya jarrabawa ta ƙasa, NECO, ta sanar da cewa za ta fitar da sakamakon jarrabawar Senior School Certificate Examination (SSCE) External ta shekarar 2025 a ranar Talata, 3 ga Fabrairu 2026. Sanarwa ta fito ne ta cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rikon kwarya ya sanya wa hannu.
Takardar ta bayyana cewa Babban Sakataren NECO kuma Shugaban Hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ne zai jagoranci fitar da sakamakon da ƙarfe 10:45 na safe. An bukaci ma’aikatan hukumar da su hallara a dakin taro da ƙarfe 10:30 domin shaida bikin.
Jarrabawar SSCE External na NECO yawanci ɗalibai masu zaman kansu ne ke rubutawa, musamman waɗanda ba sa cikin tsarin makarantu na yau da kullum. Hukumar kan shirya irin wannan jarrabawa ne domin bai wa waɗanda suka rasa damar rubutawa ko ke son gyara sakamakonsu damar samun shaidar kammala karatu.
