Majalisar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Neja ta bayyana cewa adadin daliban da aka sace daga makarantar St Mary’s Catholic Primary and Secondary School da ke Papiri, Agwara, ya ƙaru zuwa 303, bayan ƙarin tantancewa da bincike. CAN ta ce abin takaici ne cewa harin ya faru ba tare da kowanne irin umarni daga gwamnati ko hukumomin tsaro na cewa a rufe makarantu a yankin ba, sabanin ikirarin da wasu jami’ai ke yadawa bayan aukuwar lamarin.

 

Shugaban CAN na jihar, Most Rev. Bulus Yohanna, ya ce makarantar ba ta taɓa samun wasiƙa, sakon gargaɗi ko sanarwar sirri daga kowane ɓangare na gwamnati kafin harin. Bishop ɗin ya ƙara da cewa duk lokacin da aka sami barazana a baya, makarantar kan rufe ba tare da bata lokaci ba, amma wannan karon babu wani umarni — rubutacce ko na baki — daga gwamnati ko Ƙungiyar Makarantun Kuduɗi da zai nuna hatsarin da ke tafe.

 

Yohanna ya jaddada cewa jimillar waɗanda aka sace sun kai 315, ciki har da dalibai 303 da malamai 12, yana mai kira ga iyaye da al’umma su kasance cikin nutsuwa yayin da ake ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin yankin domin kubutar da yaran cikin koshin lafiya. Ya ce ya zama dole gwamnati ta daina mayar da al’amura bayan fage, ta kuma dauki nauyin gazawarta wajen kare rayukan ɗalibai da malamai.

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version