Hukumar bayar da lamunin karatu ta Najeriya, NELFUND, ta bayyana cewa ta riga ta tura N140.9 biliyan ga dalibai tun bayan buɗe shafinta a 24 Mayu 2024. Rahoton yau-da-gobe da ta fitar ya nuna cewa daga cikin 1,193,228 da suka nemi tallafin, 788,947 sun amfana, inda aka samu sabbin aikace-aikace 35,773 cikin mako ɗaya kacal.

Hukumar ta ce ta biya 262 cibiyoyi kudin makaranta, ciki har da fiye da N53.7bn a matsayin kudin rayuwa na ɗalibai da kuma wasu N88.9m na kudaden cibiyoyi. Wannan karin lamuni na nuni da yadda gwamnati ke ƙoƙarin rage wa ɗalibai nauyin karatu, tare da inganta damar samun ilimi a fadin ƙasar.

A cewar hukumar, wannan cigaba na daya daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke son yi domin fadada tsarin zuwa horon sana’o’i da fasahohi nan gaba. Wata majiya ta tabbatar da cewa kakakin NELFUND, Akintunde Sawyerr, ya ce hakan ya yi daidai da kudirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na habaka ilimin fasaha da bai tsaya ga jami’o’i kaɗai ba.

Sawyerr ya kara da cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta daidaita tsakanin ilimin boko da na fasaha domin gina ƙwararru masu iya kaiwa ƙasar mataki na gaba. Ya ce duk da cewa ba a fara tsarin vocations ba tukuna, gwamnati na aiki tukuru domin tabbatar da cikkaken shiri.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version