Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi ‘yan Najeriya 153 da suka makale a ƙasar Chadi karkashin shirin dawowa gida (Assisted Voluntary Return Programme) wanda Ƙungiyar Kula da Ƙaura ta Duniya (IOM) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya. Jirgin ASKY Airlines mai lamba CAS-AC ne ya sauke su a filin jirgin saman Murtala Muhammed, Legas, da misalin ƙarfe 12:15 na rana, ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2025.

Bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa cikin waɗanda suka dawo akwai manya 105 (maza 63 da mata 42), yara 45 (maza 25 da mata 20), da kuma jarirai uku mata. Bayan isowarsu, jami’an Hukumar Shige da Fice (NIS) sun gudanar da rajista da tantance su domin samun sahihin bayanai da sauƙaƙa musu komawa rayuwa cikin sauƙi.

NEMA ta bayyana cewa an ba wa waɗanda suka dawo taimakon gaggawa kamar abinci, ruwa, kula da lafiya, da motar daukar marasa lafiya, tare da shawarwari da goyon baya. Hukumar ta ce wannan mataki na cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na tabbatar da dawowar ‘yan ƙasa cikin mutunci da aminci, ba tare da wahala ba.

Rahoton ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko ba, domin kwanaki kaɗan da suka gabata ma, NEMA ta karɓi wasu ‘yan Najeriya 150 daga Agadez, Jamhuriyar Nijar, karkashin irin wannan shiri. Hukumar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da haɗin gwiwa da IOM da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Masu Hijira (NCFRMI) domin taimaka wa dubban ‘yan Najeriya da suka makale a ƙasashen waje su koma gida cikin mutunci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version