Hukumar Kwastam ta Najeriya, Port Harcourt Area I Command, ta samu karin kudaden shiga da ba a taba samu ba, inda ta tara N33.75bn a watan Oktoba 2025 kacal. Wannan adadi ya ninka sau uku fiye da N9.07bn da aka tara a watan Oktoba 2024. Daga watan Janairu zuwa Oktoba 2025, hukumar ta tara jimillar N247.46bn, wanda ya zarce kudin da aka tara a irin wannan lokaci na shekarar da ta gabata.

 

Kwamptrolla Salamat Aliyu Atuluku, shugabar hukumar, ta bayyana cewa sun riga sun wuce burin shekara na tara N216bn, domin sun yi sama da shi da N31bn tun kafin shekarar ta kare. Ta ce wannan cigaba ya faru ne saboda tsarin aiki mai tsari, sabbin dabarun kididdiga, da kuma himma da kiyayi na jami’an hukumar wajen aiwatar da aikinsu ba tare da sakaci ba.

 

Hukumar ta ce amfani da tsarin dijital ɗin B’odogwu ya taimaka matuka wajen duba bayanai kai tsaye, gano matsaloli cikin gaggawa, da kuma tabbatar da gaskiya da sahihancin biyan haraji daga masu shigo da kaya. Haka kuma hadin kai da sauran hukumomin tsaro da kamfanonin tashar jiragen ruwa ya rage sabani da jinkiri a lokacin sakin kaya.

 

Kwastam ta kara da cewa za ta ci gaba da sa ido wajen dakile fasa-kwauri da magudin kasuwanci, tare da tabbatar da cewa kasuwanci na halal yana tafiya cikin sauki. Atuluku ta yi godiya ga babbar hukumar kwastam da dukkan mabambantan masu ruwa da tsaki, tana mai cewa wannan ci gaban zai kara taimakawa gwamnatin tarayya wajen gina hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi da sauran manyan ayyukan raya kasa.

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version