Mutum uku sun rasu, yayin da wasu goma suka ji rauni a wani rikici tsakanin makiyaya da mazauna kauyen Dagiteri a karamar hukumar Birniwa, Jihar Jigawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da tsakar dare a ranar Laraba 08 ga Oktoba, lokacin da wasu makiyaya suka kai farmaki cikin kauyen.
Shi’isu ya ce makiyayan, dauke da baka da kibau, sun kashe mutane biyu tare da jikkata wasu bakwai. ‘Yan sanda da jami’an tsaro na Operation Salama sun isa wurin domin dawo da zaman lafiya, inda suka kama mutum bakwai tare da kwace makamai, wayoyi da wani kayan tsafe-tsafe.
Bincike ya nuna rikicin na da nasaba da mutuwar wani da ake zargi da sata wanda aka kama aka kashe a kauyen a ranar Talata. Sai makiyaya sama da 70 suka dawo a ranar Laraba domin daukar fansa, inda suka kashe mutane biyu, suka jikkata wasu da suka hada da tsofaffi, sannan suka kona babur daya suka tafi da wani.
Mazauna yankin sun bukaci gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin hana rikicin kara bazuwa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
