Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta raba tallafin kuɗi har Naira miliyan 8.4 ga mutane 18 da suka haɗa da ‘yan uwa na jami’an da suka rasu da kuma wani jami’i guda. Tallafin ya fito ne daga shirin inshora da jin daɗin ma’aikata na rundunar.

Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a, SP Abdullahi Haruna ya fitar, ta ce Kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya jagoranci rabon a hedikwatar rundunar da ke Bompai. Ya ce wannan na daga cikin umarnin Sufeto Janar na ‘yan sanda domin kula da jin daɗin jami’ai da iyalansu.

Wadanda suka amfana sun haɗa da iyalan jami’an da suka rasu, waɗanda suka jikkata ko suka samu hatsari yayin aiki. Sun nuna godiya ga rundunar bisa wannan tallafi, yayin da aka jaddada aniyar ci gaba da kula da walwalar jami’ai tare da hidima ga al’umma yadda ya kamata.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version