A karon farko bayan dakatar da ita na tsawon watanni shida, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta halarci zaman majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata.

Majalisar dattawan ta koma bakin aiki ne bayan ƙarin lokacin hutu da aka ɗan tsawaita, kuma zaman na yau ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Sanata Jibrin Barau.

Sanatar mai wakiltar Kogi ta Arewa ta shiga zauren majalisar cikin natsuwa, lamarin da ya ja hankalin ‘yan jarida da sauran ‘yan majalisa, kasancewar ita ce ta fi jawo cece-kuce a lokacin da aka dakatar da ita.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya nuna cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio — wanda ke cikin rikici da Natasha — bai halarci zaman majalisar ba. Sai dai ba a bayyana dalilin rashin halartar tasa ba.

Tun a baya dai dakatarwar Natasha ta haddasa muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan siyasa da jama’a, inda ake zargin an hukunta ta ne saboda zargin cin zarafi da ta yi wa Akpabio.

Masu lura da al’amura na ganin dawowarta za ta iya ƙara zafafa yanayin siyasar majalisar dattawa a makonni masu zuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version