Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta bayyana damuwa kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa Najeriya kaso mai yawa na kujerun aikin Hajji da aka ware mata. Hukumar ta ce matakin zai shafi dubban ƴan Najeriya da ke da niyyar zuwa aikin Hajji a shekarar 2026.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, NAHCON ta bayyana cewa Saudiyya ta sanar da cewa wuraren kwanan maniyyata da aka ware wa Najeriya a 2026 sun sauka zuwa 66,910, wanda ya haɗa da kujerun jihohi 51,513 da na jami’an hukumar, da kuma wurare 15,397 ga kamfanonin shirya tafiye-tafiye. Wannan adadi ya yi ƙasa da wanda aka saba samu a baya.
Hukumomin Saudiyya sun ce dalilin wannan ragewa shi ne Najeriya ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a shekarar 2025, inda aka bar kujeru 35,872 babu mai cikawa. Wasu daga cikin alhazai sun danganta hakan da tsadar kuɗin aikin Hajji da aka fuskanta a shekarar da ta gabata, wanda ya hana mutane da dama damar halarta.
Wannan mataki na zuwa ne a dai-dai lokacin da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni ga NAHCON da ta nemo hanyoyin rage kuɗin aikin Hajji na 2026 domin bai wa ƴan Najeriya damar samun sauƙin tafiya. NAHCON ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin Saudiyya domin ganin an sake duba wannan sabon tsarin.
