Tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya yi suka ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin APC ke aiwatarwa sun kasa rage talauci a Najeriya. Obi ya bayyana hakan ne bayan rahoton Bankin Duniya na ranar 8 ga Oktoba, wanda ya nuna cewa mutane miliyan 139 ke rayuwa a cikin talauci — sama da miliyan 87 a shekarar 2023.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a X ranar Talata, Obi ya ce cikin shekaru biyu da gwamnatin APC ke mulki, fiye da mutane miliyan 50 sun fada cikin talauci. Ya bayyana hakan a matsayin abin takaici da ke nuna yadda kasa ke kasa kare ‘yan ƙasa. Obi ya ce abin mamaki shi ne, maimakon gwamnati ta dauki matakin gaggawa, sai kawai ta yi musun rahoton da ya bayyana gaskiyar rayuwar talakawa.

Obi ya bayyana cewa duk da ikirarin aiwatar da gyare-gyare daban-daban, matsin tattalin arziki da talauci suna kara tsananta saboda rashin tsarin aiki mai kyau da kuma gazawar gwamnati wajen karkatar da kudaden kasar zuwa fannonin da za su haifar da ci gaba. Ya kara da cewa hakan ne ke sa Najeriya ci gaba da zama kasa mafi yawan talakawa a duniya.

Ya ba da shawarar cewa ya kamata a mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin da suka fi dacewa da talakawa, tare da bai wa kananan masana’antu da manoma goyon baya, saka jari a fannin ilimi da lafiya, da tabbatar da cewa kashe kudaden gwamnati na tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a. Obi ya ce, “Babu wata kasa da za ta ci gaba idan yawancin al’ummarta suna cikin talauci. Tare da shugabanci nagari, Najeriya za ta iya yin aiki daidai ga kowa da kowa.”

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version