Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dattijon ƙasa, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa ya kai shekaru 70 cikin natsuwa da salamar zuciya, yana mai cewa ya yafewa dukkan waɗanda su ka taɓa yi masa laifi tare da neman gafara a wajen wadanda shi ma ya ɓatawa. Ya bayyana hakan ne a yayin bikin cikar sa shekaru 70 da haihuwa, inda ya yi dogon nazari kan rayuwar da ya shafe cikin hidima ga al’umma da addini.

Shekarau ya ce shekaru da ya kwashe a siyasa da aiki sun koya masa darussan hakuri, juriya da rungumar kaddara. Ya bayyana cewa farin ciki da ƙalubale duk wani ɓangare ne na tafiyar rayuwa, amma darasin da ya fi ɗauka shi ne zaman lafiya a zuciya, musamman ta hanyar addini da yawan yafiya ga mutane. Ya ce ba wanda zai iya samun kwanciyar hankali sai ya koyi sassaucin zuciya da mantawa da abin da ya gabata.

A yayin jawabin, Shekarau ya yi godiya ga Allah bisa ni’imar tsawon rai, yana mai cewa ba kowa ke kaiwa shekaru irin waɗannan cikin kuzari da cikakkiyar natsuwa ba. Ya shawarci matasa da su guji fitina da son zuciya, tare da jajircewa wajen neman ilimi, adalci da mutunta juna don gina al’umma mai salama da cigaba.

Ya kammala da cewa bai taɓa sanya wata damuwa a ransa, har ta hanashi bacci ba, domin a cewarsa a duk wani lokaci yana miƙa al’amuransa ga Allah. Shekarau ya bayyana wannan matsayin nasa a matsayin asalin kwanciyar hankali da ɗan Adam ke nema, yana mai jaddada cewa “duk inda zuciya ta huta, can ne rayuwa ta gaskiya take.”

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version