Sojojin Rundunar shiyya ta 8 ta Nigerian Army da ke Sokoto sun samu babban nasarar kashe fitaccen ƙasurgumin ɗan fashi da makami, Kachalla Kallamu, a yankin Sabon Birni. Rahotanni sun nuna cewa an kashe Kallamu ne tare da wani babban mai ba Bello Turji kayan aiki a wani samame na musamman da aka kaddamar da sassafe a kusa da kauyen Kurawa.

Wata majiya daga sojoji da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana cewa Kallamu, wanda tsohon mataimaki ne na Bello Turji, ya hadu da ajalinsa ne bayan bayanan sirri da rundunar ta samu tare da haɗin guiwar jami’an sa-kai. Kallamu, wanda ya fito daga Garin-Idi a Sabon Birni LGA, ya shahara da kai hare-hare da addabar jama’a a yankin kafin ya gudu zuwa Kogi a watan Yunin 2025 sakamakon wani artabun da sojoji suka yi da tawagarsa.

Bechi ta tattaro cewa mutanen yankin da dama, ciki har da Mai Ba Gwamnan Jihar Sokoto Shawara kan Harkokin Tsaro, Kanal Ahmad Usman (rtd), na ci gaba da murnar wannan nasara da sojoji suka samu. Majiyar ta kara da cewa haɗin kan al’umma wajen bayar da bayanan sirri ya taka rawar gani wajen cimma wannan gagarumar nasara da rundunar 8 Division ta samu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version