Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya ayyana dokar gaggawa kan harkokin tsaro a fadin kasar nan sakamakon karuwar sace-sace, hare-hare da ta’addanci a jihohi daban-daban. Ya bayar da umarnin a dauki karin jami’an ‘yan sanda 20,000 wanda hakan zai kai yawan wadanda ake shirin dauka zuwa 50,000, tare da amincewa da amfani da sansanonin NYSC a matsayin cibiyoyin horaswa na wucin-gadi. Haka kuma ya bukaci jami’an da aka janye daga kula da manyan mutane su samu horaswar gaggawa domin tura su yankunan da ake fama da kalubalen tsaro.

Tinubu ya kara baiwa rundunar DSS ikon tura masu gadin dazuzzuka domin fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ke boye a dazuka, tare da umarnin kara daukar ma’aikata domin karfafa wannan yaki. Ya godewa jami’an tsaro kan kubutar da dalibai 24 a Kebbi da masu ibada 38 a Jihar Kwara, tare da bayyana aniyar gwamnati na ci gaba da kokarin ceto daliban da ke tsare a Jihar Neja. Ya kuma bukaci Majalisar Dokoki ta yi garambawul ga dokoki domin baiwa jihohi damar kafa ‘yan sandan jiha idan bukata ta taso.

A tattaunawarsa da manema labarai, Shugaban ya shawarci hukumomin kananan hukumomi, masallatai da coci-coci su kara tsaurara matakan tsaro, musamman a yankunan da ake fuskantar barazana. Bechi Hausa ta tattaro cewa Tinubu ya kuma jaddada cewa gwamnati ta kirkiro Ma’aikatar Kiwo domin warware rikicin manoma da makiyaya, inda ya bukaci kungiyoyin makiyaya su daina kiwo a fili, su mika makamai ba bisa ka’ida ba, kuma su rungumi tsarin ruga domin zaman lafiya mai dorewa.

Shugaban kasa ya jajanta wa rundunar soji bisa rasa jarumai ciki har da Birgediya Janar Musa Uba a yayin aikin yaki da ta’addanci. Ya yi kira ga ‘yan kasa kada su firgita, su rika bayar da rahoton abubuwan da ake zargi, tare da hadin kai da hukumomin tsaro. Ya tabbatar da cewa gwamnati na da cikakken kuduri na kare rayuka da dukiyoyi, tabbatar da hadin kai da dawo da zaman lafiya a dukkan bangarorin kasar. “Allah Ya ci gaba da kare Najeriya da kuma kiyaye dakarunmu,” in ji shi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version