Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya aika wa Majalisar Dattijai da wasiƙa yana neman amincewar ta domin tantancewa da tabbatar da sabbin shugabannin hafsoshin tsaro da ya nada a baya-bayan nan. An karanta wasiƙar ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata 28 ga Oktoba ta bakin shugaban majalisar, Godswill Akpabio.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana sunayen waɗanda ake son a tabbatar, ciki har da Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Manjo Janar Waheedi Shaibu; Babban Hafsan Rundunar Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas; Babban Hafsan Rundunar Sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke; da kuma Daraktan Leken Asiri na Tsaro, Manjo Janar Emmanuel Undiendeye.

Bayan karanta wasiƙar, Akpabio ya umurci a mika sunayen waɗanda ake son a tabbatar ga Kwamitin Majalisar Dattijai domin gudanar da bincike da tabbatarwa a mako mai zuwa. Wannan na zuwa ne bayan ganawar sirri da Tinubu ya yi da sabbin hafsoshin tsaro a fadar shugaban ƙasa ranar Litinin.

Ana ganin wannan sabon mataki na shugaban ƙasa a matsayin ɓangare na ƙoƙarin sabunta tsarin tsaro da inganta haɗin kai tsakanin rundunonin sojoji domin tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version