Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai farfaɗo da matatun man ƙasar da suka jima ba sa aiki, tare da tabbatar da cewa sun koma aiki yadda ya kamata.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, lokacin da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG) ta kai masa ziyara a fadarsa.

Da yake mayar da martani kan matsalolin da ƙungiyar ta gabatar, shugaban ya jaddada cewa dole ne matatun su kasance masu riba tare da samar da amfanin da aka gina su domin samarwa.

Tinubu ya ce ya ɗauki alhakin gyara kadarorin ƙasar da matsalolin da gwamnatocin baya suka bari, yana mai cewa duk abin da ya faru a baya, yanzu alhakinsa ne ya gyara abubuwan tare da tabbatar da cewa suna aiki yadda ya kamata domin amfanin mafi yawan al’ummar ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version