Wasu yan ta’adda sun kutsa Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a jihar Niger, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata a tsakanin ƙarfe 2 zuwa 3 na dare, a ranar Juma’a, 21 ga Nuwamba 2025. Har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda aka sace ba, inda majiyar cocin Katolika ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce za ta fitar da cikakken bayani daga baya. Haka zalika, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce za ta bayyana bayanan da suka tattara nan gaba.

Harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan makamancin shi a Maga, jihar Kebbi, inda aka yi garkuwa da dalibai 25, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a game da tsaron makarantu a Arewa. A lokaci guda, hukumomi sun rufe fiye da makarantu 50 a jihar Kwara sakamakon barazanar ‘yan bindiga, yayin da shugabannin tsaro da hukumomi ke ƙoƙarin tantance adadin mutanen da aka yi awon gaba da su a harin na Agwara.

Lamarin ya kuma zo a daidai lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soke tafiye-tafiyensa zuwa Afirka ta Kudu da Angola domin jagorantar matakan gaggawa kan tsaro. Wannan karin hari ya sake jaddada yadda rikicin tsaro ke ta’azzara a yankunan Arewa, musamman a makarantu, abin da ke ƙara tayar da hankalin iyaye da al’umma gaba ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version