Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun ƙona sakatariyar jam’iyyar African Democratic Congress a garin Ubima da ke ƙaramar hukumar Ikwerre a jihar Rivers State. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis gabanin zuwan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi.
Rahotanni sun ce ‘yan daban sun kai hari da harbe-harbe tare da ƙona ofishin jam’iyyar kafin su sake bayyana da safe, inda suka kafa shingen bincike a kan hanyar Omuawa zuwa Ubima, suna hana motocin da ke ɗauke da tutar ADC shiga garin.
Mazauna yankin sun ce jami’an tsaro da aka tura wurin sun yi nasarar tarwatsa ‘yan daban tare da dawo da zaman lafiya. Sai dai kakakin ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ba ta amsa kira ko saƙonnin da aka aike mata ba domin tabbatar da faruwar lamarin.
