Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 105 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a wani gagarumin samame da ta gudanar a sassan jihar. Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Dutse, inda ya ce jami’an tsaro sun gudanar da sintiri a ko’ina don kawar da miyagun kwayoyi daga cikin al’umma.

A yayin samamen, ‘yan sanda sun kwace nau’ikan miyagun kwayoyi sama da 5,000, ciki har da tabar wiwi da kwayoyi masu sa maye. Daga cikin kayan da aka gano akwai Exol guda 2,541, D-5 guda 1,146, Tramadol guda 270, da kuma fiye da dubu ɗaya na wraps ɗin wiwi da guda ɗaya cikakke. Haka kuma an kwace Diaxer guda 269, Pregabalin guda 153, da Farin Malam guda 82, tare da wasu kwayoyi irin su Diazepam, Vegakris da Calidon’s.

Bugu da ƙari, rundunar ta gano kuɗi Naira 92,460 daga hannun waɗanda ake zargi, tare da wasu abubuwan maye kamar “rubber solution,” “suck and die,” da giya. SP Adam ya ce wannan samame babban saƙo ne ga masu hannu a safarar miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa rundunar ba za ta yi sassauci ba wajen ci gaba da wannan yaki.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba ‘yan sanda goyon baya ta hanyar bayar da bayanai kan duk wata mummunar aiki a yankunansu. Ya ce hadin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen nasarar yaƙi da safarar kwayoyi a jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version