Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hare-hare a ranar Asabar kan sansanin ‘yan gudun hijira da ke Damasak da kuma ofishin ‘yan sanda na Nganzai a jihar Borno, inda suka kashe jami’an tsaro biyar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Nahum Daso, ya ce maharan sun kai farmaki da makamai masu ƙarfi ciki har da rokoki, inda suka yi yunƙurin kwace garin amma jami’an tsaro suka dakile su. Ya ce jami’an ‘yan sanda huɗu sun mutu a harin Nganzai, yayin da wani mafarauci ya rasa ransa a Damasak.

Ya ƙara da cewa maharan sun lalata wani ɓangare na ofishin ‘yan sanda tare da ƙona wata motar sulke da ba ta aiki. Sai dai haɗin gwiwar jami’an tsaro da na sa-kai sun samu nasarar fatattakar maharan, inda kwamishinan ‘yan sanda ya tura ƙarin jami’ai domin ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version