Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta sanar da fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya daga ƙarfe 12:00 na dare a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026, saboda shirin da gwamnatin tarayya ke yi na dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus-alawus da aka amince da shi bayan yajin aikin 2025.

Shugaban NARD, Dakta Shuaibu Ibrahim, ya bayyana cewa matakin gwamnati na soke tsarin alawus ɗin ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma a baya, yana mai cewa hakan ne ya tilasta musu komawa yajin aiki. Ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taron majalisar zartarwa na ƙasa da aka gudanar ta yanar gizo.

Ƙungiyar ta buƙaci a dawo da tsarin alawus ɗin nan take tare da biyan dukkan basussukan albashi da alawus na watanni 19, da kuma kammala biyan kuɗin horar da likitoci na shekarar 2026. Ta kuma gargaɗi cewa yajin aikin na iya kawo tsaiko ga ayyukan asibitocin gwamnati da kuma ƙara matsin lamba ga tsarin lafiya a ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version